1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsinke layin intanet da na tarho a Gaza

Abdourahamane Hassane
January 19, 2024

An tsinke layin tarho da intanet a yankin zirin Gaza yau tsawon mako guda ,a cewar NetBlocks, wata kungiyar da ke saka ido kan hanyoyin sadarwa na duniya.

https://p.dw.com/p/4bU3y
Hoto: DW

 Tsinkewar intanet din ita ce mafi tsayi da aka samu tun da aka soma yakin na Gaza a cikin watan Oktoban da ya gabata ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (Ocha). Ya ce rashin intanet din na hana mazauna Gaza samun mahimman bayanai ko kuma kiran agajin farko. A halin da ake ciki  ma'aikatar lafiya ta Hamas,ta ce sama da mutane dubu 24, mafi yawancin mata,da yara kanana, suka mutu ,yayin da sama da dubu sittin suka jikkata kawo yanzu tun lokacin da aka fara  yakin.