Sabbin hare-haren Isra'ila a Kudancin Gaza
January 19, 2024Da sanhin safiyar Juma'a 19.01.2024, masu aiko da rahotanni sun shaidar da cewa an kai hare-hare ta sama a wani babban gari da ke kudancin zirin Gaza da ake kira Khan Younes wanda Isra'ila ta bayyana a matsayin mafakar shugabannin kananan hukomomin Falasninawa da ke karkashin kungiyar Hamas.
Karin bayani: Majalisar EU ta bukaci a kawo karshen luguden wuta na din-din-din a Gaza
Kungiyar agaji ta Red Crescent da ke yankin Falasdinu ta yi Allah wadai da harba makami mai linzami a kusa da asibitin al-Amal da ke dan karamin yankin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wadansu a cikin daren Alhamis wayewar Juma'a inji hukumar Wafa ta Falasdinu a rahoton da ta fitar.
Karin bayani: Antony Blinken ya yi tozali da Mahmud Abbas kan rikicin Hamas da Isra'ila
Daga nasu bangare sojojin Isra'ila sun ce sun halaka 'yan ta'adda da dama a Khan Younes tare da yin ikirarin cewa sun isa yanki mafi girma na kudancin Gaza tun lokacin da suka kai farmaki ta kasa.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yanayin jin kai na ci gaba da fuskantar mawuyacin hali a zirin Gaza inda kusan kashi tamanin cikin dari na al'umma suka rasa matsugunensu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas. Hukumar ta kuma yi shailar barkewar sabbin cutuka a dan karamin yankin na Falasdinu ciki har da ciwon hanta wanda kawo yanzu aka gano mutane 24 masu dauke da kwayoyin cutar.