1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi jana'izar shugaban Hamas a Iran

August 1, 2024

A wannan Alhamis din ce, shugaban addinin kasar Iran, Ayotollah Ali Khamenei ya jagoranci jana'izar shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran.

https://p.dw.com/p/4izBD
Jana'izar shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh a Tehran
Jana'izar shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh a TehranHoto: Iranian Leader Press Office/Anadolu/picture alliance

Shugaban addinin kasar Iran, Ayotollah Ali Khamenei ya jagoranci jana'izar shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh bayan da ya gamu da ajalinsa a wani harin da ake zargin Isra'ila ta kai kan gidansa a birnin Tehran. Ana sa ran, Ayotollah Ali Khamenei ya kara jagorantar taron addu'o'in birne marigayin a birnin Doha na kasar Katar, bayan ya sha alwashin daukar fansa a kan kisan.

Karin bayani: An kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran 

Dubban mutane ne dauke da hotunan Haniyeh da kuma tutocin Falasdinu suka yi jerin gwano domin bin sallar gawar marigayin a Jami'ar Tehran. A ranar Laraba ce aka tabbatar da mutuwar Ismail Haniyeh da wani dogarinsa yayin da yake ziyara a Iran domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar.

Karin bayani: Martanin kasashen duniya bayan kisan Ismail Haniyeh

Wasu kasashen duniya dai na ci gaba da martani kan kisan jagoran na Hamas, sai dai Isra'ila har yanzu bata ce uffan ba game da harin na birnin Tehran.