Harin Isra'ila kan makaranta ya halaka Falasdinawa 30
July 27, 2024Adadin mutane da suka rasa rayukansu a wani harin da Isra'ila ta kaddamar ranar Asabar a kan wata makaranta a zirin Gaza ya kai 30.
Hukumomin ma'aikatar lafiya ta Falasdinu sun ce makarantar mafaka ce ga wadanda suka rasa gidajensu, sai daiIsra'ila ta ce ta hari masu dauke da makamai ne da ke amfani da muhallin.
Netanyahu ya gana da Shugaba Joe Biden a Amurka
Ofishin yada labarai da gwamnatin Hamas ke iko da shi ya ce yara 12 da kuma mata takwas na cikin wadanda harin ya ritsa da su a tsakiyar garin Deir Al-Balah.
Sai dai sojojin Isra'ila da suka kai harin sun ce 'yan kungiyar Hamas ne suka halaka ba fararen hula ba, sun kara da cewa sun dauki matakan da suka rage barazana ga fararen hula yayin farmakin.
Netanyahu ya kai wa sojojin Isra'ila ziyara a Gaza
Da ya ke martani kan wannan harin babban jami'in da ke kula da harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell, ya yi kira da a nemi mafitar siyasa domin kawo karshen abinda ya kira 'hauka' da ke faruwa a Gaza.