1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu zai kashe Tiriliyan biyar kan tallafin fetur

Ubale Musa Abdoulaye Mamane(Sulaiman Babayo)
June 5, 2024

Bayan share tsawon lokaci ana takaddama kan batun janye tallafin man fetur a Najeriya, a karon farko cikin shekara guda gwamnatin tarayya ta sanar da sake biyan tallafin man fetur din kasar ga al'umma.

https://p.dw.com/p/4ggaR
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Gwamnatin Najeriya ta sa kafa ta shure  tallafin man fetur  din kasar a karon farko gwamnatin tarayya ta ce tana biyan tallafin man fetur yanzu haka, kana ministan kudin kasar Wale Edun ya ce Najeriyar na hasashen biyan Naira Triliyan 5.4 a matsayin kudaden tallafin man fetur din da al'ummar kasar suka amfana..

A shekarar da tagabata gwamnatin Najeriya ta biya fiye da  Naira Triliyan 3.6 da kasar ta biya a matsayin kudin tallafin mai bayan da ta sanar da cewa ta jefar da kwallon mangwaro ta huta da kuda.

Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a bakunan 'yan Najeriya da dama musamman ma masanan tattalin arziki da masu siyasa

Masu ababen hawa na dakon samun mai daga dogon layi a Najeriya
Masu ababen hawa na dakon samun mai daga dogon layi a Najeriya Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Karin bayani : Cire tallafin mai ya haifar da cece-kuce a Najeriya

Babban makasudin zare tallafin man fetur din tun a ranar farko ta karbar rantsuwar shugaban Najeriya Bola Tinubu na zaman hanya guda ta neman ceto tattalin arziki da mahukunta suka ce na kan hanyar rushewa.

Zare tallafin man ya sa an fuskanci  tashin farashin man  daga Naira 167 kan kowace lita kafin zartar da hukuncin zuwa Naira 800 a mafi yawan kasar a yanzu, hakan ya kara ruda 'yan Najeriya da ke biyan hajjar man a cikin tsada, amma kuma ake sanar da su cewa har yanzu ana ci gaba da biyan kudin tallafi daga aljihun gwamnati.

Karin bayani :  Najeriya: Martani kan tallafi ga talakawa

Tarzoma kan janye tallafin man fetur a Najeriya
Tarzoma kan janye tallafin man fetur a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Gwamnatin Najeriya a yanzu na nuna alamun kasancewa cikin tsaka mai wuya bis abatun na zare tallafin man fetur din, duba da karin farashin man da ya jefa kasar cikin sabon rikici wanda har yanzu gwamnatin Najeriya ke neman hanyoyin warware kullin zaren da ya sarke a tsakanta da 'yan kwadago.

Karin bayani : Najeriya: Cece-kuce kan tallafin iyalai

A yayn da a share guda kuma da ci gaba da biyan kudin tallafin na nufin kara shigar gwamnati a wani matsin rashin kudin da masu mulkin ke fatan amfani da su wajen ingantar raya kasa.