1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Ana zaben majalisar kasa a Siriya

July 19, 2020

Al'umar kasar Siriya na zaben 'yan majalisar dokokin kasa, zaben da ke zuwa yayin da kasar ke fama da matsi daga kasashen duniya da tarrnaki na tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/3fY7Y
Parlamentswahlen in Syrien I Archivbild
Hoto: picture-alliance /AP/Syrian Presidency

Sama da rumfunan zabe dubu 7,400 ne suka bude a fadin yankunan da ke a hannun gwamnatin kasar ta Siriya, ciki har da wani yanki da 'yan adawa ke da karfi a cewar hukumar zaben kasar.

Ana kuma sa ran jam'iyyar Baath ta Shugaba Bashar al-Assad, ta lashe akasari daga cikin kujeru 250 na majalisar.

Wannan ne dai zabe karo na uku da ake yi yayin da kasar ta Siriya ke fama da yaki cikin tsukin shekaru tara.

Aakalla mutumu guda ya rasa ransa jajibirin zaben wani ma ya jikkata sakamakon tashin boma-bomai a birnin Damascus.