Shirin tuhumar Trump kan laifin badala
March 31, 2023Mr. Trump zai fuskanci shari'a bisa zargin bayar da wasu makudan kudade a matsayin toshiyar baki ga wata shahararriyar mai fina-finan batsa, kafin zabensa da aka yi a shekarar 2016. Ya dai bayar da kudaden ne domin hana ta magana a kan zargin da ya fito fili a kansa a wancan lokaci dangane da mu'amalar da ya yi da matar mai suna Stormy Daniels.
Babban mai gabatar da kara a kotun birnin Manhattan, Alvin Bragg ya ce, tuni alkali ya sanya hannu kan takardar tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban na Amirka Donald Trump. Amma tsohon shugaban tare da dumbin magoya bayansa, na bayyana tuhumar a matsayin bita-da-kullin siyasa, ganin ya shirya wa takara a zaben Amurkar da za a yi a badi.
Abin da ya fito fili shi ne, wannan wata babbar guguwa ce da ke iya shafar siyasar tsohon shugaban na Amurka Donald Trump, duk da yake dai mutum ne da ke fama da zarge-zarge a siyasarsa. Su ma masana harkokin shari’a, suna bayyana fahimtarsu kan wannan dambarwa da ke da nauyi ta fuskar doka, kasancewar wanda abin ya shafa tsohon shugaban kasa ne.
Ita dai matar mai harkar fina-finan badala ko batsa bayanai na cewa, ta karbi tsabar kudi ne da suka kai dala dubu 130, makonni kafin zaben shugaban kasa da ya dora tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan karaga. Bayanai sun nuna cewa lauyan Donald Trump Michael Cohen, shi ne ya mika wa matar wato Stormy Daniels wadannan kudade, kafin daga bisani Mista Trump ya biya shi. A baya ma dai lauya Michael Cohen, ya shaida wa majalisar dokokin Amurkar wannan bayani da ma alkali a birnin New York.
Cikin kwanakin da ke tafe, ake sa ran fara sauraron wannan kara da ake ganin tsohon shugaban na Amurka Donald Trump zai shiga wani babi na sabon rikici. Akwai kararraki daga wasu matan da ke jiran tantancewa kafin a shigar da su gaban shari'a a game da cin zarafi da lalata da matan suka zargi Mista Trump ya yi da su.