Duniya na fuskantar annobar coronavirus
March 19, 2020Talla
A kasashe da dama an sami karuwar mace mace a sakamakon yaduwar cutar coronavirus inda wasu kasashe suka rufe iyakokinsu domin dakile yaduwar cutar.
Kasar Italiya a cewar Firaminista Giuseppe Conte za a tsawaita wa’adin rufe iyakoki da takaita zirga zirgar jama’a.
Mutanen da suka kamu da kwayar cutar sun hauwa mutum 200,000 a fadin duniya baki daya.
A Jamus shugabar gwamnati Angela Merkel ta bayyana halin da aka shiga a kasar a matsayin kalubale mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu
Kasashen Afirka ma ba a bar su a baya ba wajen daukar matakan rufe iyakokinsu.