Matsayar AU a taron kan sauyin yanayi
September 6, 2023Yayin da ake shirin karkare taron kolin na kwanaki uku kan sauyin yanayi karo na farko da shugannin kasashen Afrika suka shirya a kasar Kenya, shugaban kasar Kenya mai masauki baki Willian Rutu ya ce ko baya ga nahiyar Afrika matakan da suka yanke shawarar dauka za iya tasiri a duniya baki daya domin bullo wa lamarin sauyin yanayi da ke da ke haddasa ibtila'o'i ciki har da ambaliyada kuma fari.
Karin bayani: Kasashen Afrika na taro kan sauyin yanayi
A mairaincan nan wannan Laraba (06.09.2023) shugabannin kasashen za su fitar da sanarwar bai daya wace za su gabatar a taron koli na duniya kan sauyin yanayi na COP28 wanda za a gudanar a Hadaddiyar Daular Larabawa a karshen watan Nowamba mai zuwa.
Karin bayani: Illar sauyin yanayi a Afirka
A cikin sanarwar ana sa ran shugabannin za su bukaci kasashe masu karfin masana'antu da su duba yiwuwar yafe wa kasashen Afrika basusuka a matsayin diyyar dumamar yanayin da suke haddasawa.
Karin bayani: Bukatar yafe bashi ga Najeriya da kasashe matalauta