Jim Mattis ya nesanta kansa daga kalaman Trump.
February 19, 2017Sakataren tsaron Amirka Jim Mattis, ya nesanta kansa daga kalaman Shugaban Amirka Donald Trump da ya ce kafafen watsa labarai makiyan al'umar Amirka ne. A yayin ziyararsa a yankin larabawa, sakataren tsaron na Amirka ya ce ba shi da wata matsala da 'yan jaridu ko kafafen watsa labarai.
Mr. Jim da ke nesanta kan nasa da kalaman Mr Trump dai, ya ce ana samun wasu lokuta marar dadi da 'yan jaridu, amma fashi 'yan jaridun, abokai ne na tafiya ala-kulli halin. A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya sake sukar wasu daga cikin manyan kafofin yada labaran Amirka, wadanda ya bayyana su da cewar makiya ne na Amirkawa. Sakataren tsaron na Amirka Jim Mattis ya kuma soke ziyara kasar Afghanistan da ya tsara a wannan Lahadi don ganawa da Shugaba Ashraf Ghani, saboda rashin kyawun yanayi.