Babu wanda ya tsira da rai a hadarin jirgin sama a Brazil
August 10, 2024Talla
Shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil da sauran jami'an kasar sun yi hasashen cewa ta yiwu dukannin fasinjojin da kuma ma'aikatan jirgin da hadarin ya rutsa da su sun rigamu gidan gaskiya. Faya-fayan bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda jirgin kamfanin Voepass Linhas Areas, ya rikito daga sama zuwa kan wasu rukunin wasu gidaje.
Karin bayani: Hadarin jirgin sama a Brazil
Jami'an kwana-kwana da kuma ma'aikatan agaji na gudanar da aikin ceto yayin da wasu jami'an suka ce sun gano na'urar bayanai ta cikin jirgi wato black box a turance. Gwamnatin Jihar Sao Paulo ta mika jajjenta tare da goyon baya ga iyalan wadanda da hatsarin ya rutsa da su.