1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangladesh: An rantsar da Hasina a wa'adi na 4

January 11, 2024

An rantsar da Sheikh Hasina a matsayin Firanministar Bangladesh a wa'adi na hudu a jere, kasa da mako guda da jam'iya mai mulki ta lashe zaben 'yan majalisar kasar.

https://p.dw.com/p/4b99V
Firanministar Bangladesh, Sheikh Hasina
Firanministar Bangladesh, Sheikh HasinaHoto: Munir Uz Zaman/AFP/Getty Images

Hasina dai ita ce Firanminista ta farko a tarihin Bangladesh da aka zaba sau hudu a jere. Shugabar mai shekaru 76 da haihuwa ta sha rantsuwar kama aiki ne a ofishin shugaban kasa, Mohammed Shahabuddin tare da majalisar ministocinta.

Tun da fari dai, babbar jam'iyar adawa ta kasar BNP ta tsohuwar Firanminista Khaleda Zia ta kaurace wa zaben saboda fargabar rashin gudanar da sahihin zabe.

Karin bayani: Bangladesh: Sheikh Hasina ta lashe zabe

Dama jam'iyar ta dade ta na neman a gudanar da zabe karkashin gwamnatin rikon kwarya, sai dai kuma jam'iyyar Hasina ta Awami League Party ta yi watsi da bukatar, inda ta ce hakan ya saba wa kudin tsarin mulkin kasar.