1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin Duniya zai tallafa wa kasashen Afirka

May 3, 2019

Bankin duniya, ya ce ya shirya wani shirin bai wa kasashen Afirka rance da zai taimaka masu wajen yaki da talaucin da ke addabarsu a halin da ake ciki.

https://p.dw.com/p/3HuOv
David Malpass
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/E. Vucci

Sabon shugaban bankin na duniya, David Malpass, shi ne ya shaidar da hakan a ranar Juma'a bayan kammala wani ran gadin da ya kai wasu kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara.

A ranar Litinin ne dai Mr. Malpass, ya fara ziyarar kasashen Madagaska da Ethiopia wato Habasha da kuma kasar Mozambik.

Bankin na duniya ya yi alkawarin bullo da wani shiri na musamman da yace na yaki da talauci ne tsantsa cikin kasashen na Afirka.

Dama bankin na da wani asusu na musamman da ke bai wa kananan kasashen tallafi.