Shugaban Belarus ya gargadi EU
August 19, 2020Kasashen Faransa da Jamus da kuma kungiyar EU, sun fito karara sun ce ba su gamsu da yadda Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus din ke tunkarar masu adawa da sakamakon zaben da ya ba shi nasara ba. Kasashen na Turai dai sun kuma yi kira ga kasar Rasha wacce ke goyon bayan shugaban Belarus din, kan ta daure ta sanya shi ya yi amfani da tattaunawa a maimakon kamu da kuma muzgunawa masu zanga-zangar adawa da shi.
Wolfgang Schäuble shi ne kakakin majalisar dokokin Jamus ta Bundestag: "Dole ne Turai ta fayyace cewa za ta yi amfani da duk abin da ya dace domin inganta hakkin dan Adam da dimukuradiyya ta hanyar lumana. NahiyarTurai ba ta da niyyar karkata akalar mulki, amma dai tana so ta nuna cewa wani nauyi ya rataya a wuyanta na kula da makwabtanta, kuma wannan wani abu ne da ya kamata Turai ta nuna a yanzu. Idan zamanin mulkin wani dan kama karya ya kusa karewa, zai fi kyau a nemi hanya mai bullewa ba tare da karin tashin hankali ba."
A halin da ake ciki dai Tarayyar Turan na nazarin matakai kwarara da za ta dauka, domin ganin ba ta zurawa rikicin na Belarus ido ba, duk da cewa shugaban baya cikin kungiyarta amma kasarsa ta Belarus na cikin nahiyar Turai. A kan haka nema firaministan Netherlans ya yi kira ga EU din, da ta bijirewa sakamakon zaben ranar tara ga watan Agusta da ya ba Lukashenko damar yin mulki karo na shida bayan ya kwashe shekaru 26 a kan wannan kujera.
Jagorar adawar Belarus Sviatlana Tsikhanouskaya da tuni ta yi watsi da sakamakon zaben, ta shiga taron na EU ta hanyar bidiyo daga kasar Lithuania, inda take samun mafaka, ta yi jawabi tana mai cewa: "Ya ku shugabannin Turai, a yau makonni biyu ke nan a jere kasata take nuna dawa da yin karan tsaye ga tsarin mulki a wurin zaben shugaban kasa. Zaben ranar tara ga watan Agusta babu abin da ke cikin shi in ba magudi da damafara ba, wadanda suka fito neman hakkinsu kuma ana lakada musu duka da kuma daure wasunsu ba bisa ka'ida ba. Gwamnatin da idonta ya rufe na neman dawwama kan mulki."
Sai dai jim kadan bayan jagorar adawar Belarus din ta kammala kai korafin Shugaba Lukashenko gaban shugabannin kungiyar ta EU, sai kasar Chaina a karon farko ita ma ta shiga cikin maganar, inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasashen ketare Zhao Lijian ya ce kasarsa na son a bar Belarus ta magance matsalarta da kanta: "Mun gamsu cewa akwai abubuwa masu sarkakiya da ke faruwa a Belarus, a matsayinta na abokiyarmu ba za mu zauna mu zuba idanu ana mata cinne kuma mu rungume hannunmu. Mun gamsu kuma mun amince cewa Belarus za ta iya magance rikicin siyasar nan ita da kanta.''
Irin wannan goyon bayan da Shugaba Alexander Lukashenko ke samu daga kasar Rasha da kuma Chaina ne, suka sanya shi bayyana cewa ya kamata kasashen Turai su fitar da bakinsu daga rikicin siyasar kasarsa, yana mai cewa Jamus da Faransa na da matsalolinsu na cikin gida, kuma zai yi kyau su mayar da hankalinsu wurin gyara gidansu a maimakon sanya masa kahon zuka.