Blinken ya kammala ziyara a Gabas ta Tsakiya da Asiya
November 10, 2023Rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas a zirin Gaza shi ne batun da mamaye ziyarar jami'in diflomasiyyar inda ya yawaita mika sakonnin tare da jaddada goyon bayan Amurka ga Isra'ila.
Karin bayani: Blinken ya gana da shugaban Falasdinawa
Da yake magana a gaban manema labarai jim kadan kafin ya bar birnin New Delhi, mista Blinken ya yi maraba da matakin Isra'ila na tsagaita buda wuta na dan lokaci domin ba da damar isar da kayan agaji zirin Gaza, sai dai amma kuma ya ce har yanzu da sauran rina a kaba a game da ba da kariya ga Falasdinawa fararen hula.
Karin bayani: Isra'ila ta yi watsi da tsagaita wuta a Gaza
Ko baya ga rikicin Gaza, jami'in diflomasiyyan na Amurka da hukumomin Indiya sun yi tsokaci kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da ta jibanci manyan tsare-tsare ta fuskar kasuwanci domin dakile yunkurin China na mamaye kasuwannin yankin Asiya da tekun Pacifik cikin yanayi na yake-yake.