Bukukuwan Babbar Salla a kasashen duniya
August 23, 2018Talla
Duk da yanayin kuncin rayuwa da babbar sallar ta bana ta samu al'ummar Musulmi a ciki, an gudanar da shagulgulan sallar cikin annashuwa da yarda da kaddarar Ubangiji. Kamar yadda aka saba, an dauki tsauraran matakan tsaro a sassa daban-daban, inda a birnin Kano na Najeriya ma aka tsaurara matakan tsaron saboda hawa da masarautar Kano kan shirya a kowace shekara, inda bikin yake kara armashi.