1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Xi da Putin a Uzbekistan

Zainab Mohammed Abubakar
September 15, 2022

A ganawarsu ta farko tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, Shugaba Xi Jinping na takwaransa da Rasha Vladimir Putin a sun sake jaddada hadin kai da goyon bayansu ga juna.

https://p.dw.com/p/4Gwbr
Russland | Wirtschaftsforum in Wladiwostok | Xi Jinping und Wladimir Putin
Hoto: Sergei Bobylev/TASS Host Photo Agency/dpa/picture alliance

Shugabannin kasashen biyu sun gana ne a bangaren taron majalisar shugabannin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 22 a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan.

A farkon taron, Putin ya godewa Beijing dangane irin goyon bayan da take bai wa Moscow a kan rikicinsu da Ukraine, inji majiyar kafofin yada labaran Rashar.

Xi a nashi bangaren kamar yadda kafar yada labaran Beijing ta ruwaito, ya jaddada cewar, Chaina na shirye wajen mara wa Rasha baya a kan batutuwa da suka hada kasashen.