1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta yi wa Koriya ta Arewa tayin sulhu

November 26, 2022

Shugaban kasar Cina ya aika sakon neman fahimtar juna a tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa, kwanaki kalilan bayan wani gwajin makami da ya tayar da hankalin kasashe.

https://p.dw.com/p/4K7e8
Shugaba Xi Jinping na kasar ChinaHoto: Jack Taylor/AFP/Getty Images

Shugaba Xi Jinping na kasar China, ya shaida wa takwaransa Kim Jong Un na Koriya ta Arewa cewa a shirye yake da su hada kai domin samun zaman lafiya a tsakaninsu da ma duniya baki daya.

Sanarwar shugaban na China dai ta zo ne kwanaki bayan Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami da ke cin dogon zango, makamin da aka ce ya fi sauran wadanda Koriyar ta yi ta harbawa a baya.

A sakon da ya fitar dai, Shugaba Xi Jinping na China, ya ce abin da yake so shi ne samun daidaito da fahimtar juna a tsakninsu saboda ci gaban yankinsu da ma samun lumana a sauran kasashen duniya.