Corona ta kashe dubban tsoffi a Birtaniya
April 18, 2020Talla
Adadin rayukan da cutar Corona ta salwanta a gidajen kula da sun Birtaniya kadai, sun kai akalla 7,500, ninki biyar ke nan daga alkaluman da hukumomi suka kiyasta. Gidauniyar Care England, wadda ta hada kananan gidajen kula da gajiyayyu a Birtaniya, ta shaida wa jaridar Daily Telegraph, cewar tsoffin da suka wannan adadin sun mutu ne daga ranar daya ga wannan wata zuwa halin da ake ciki.
Dama a farkon wannan makon ne, hukumomi a Birtaniyar suka ce dattawan dubu daya da 400 cutar ta kashe. A halin da ake ciki dai akwai mutum dubu 14 da 576 da corona ta yi sanadin salwantarsu a kasar.