Sassauta dokar kulle a kasashen duniya
May 7, 2020Talla
Al'amura sun tsaya cak haka ma harkokin kasuwanci sun raunana a duniya, sakamakon dokar zaman gida da kasashen duniya da dama suka assasa domin rage yaduwar annobar cutar coronavirus ko kuma COVID-19 da ta yi wa duniya tsinke.
Koda yake a kasashen Afirka misali Najeriya, masana kiwon lafiya na ganin tamkar an yi garaje wajen saukaka dokar zaman gidan. Matsalar da aka fi fuskanta a nahiyar Afirkan dai shi ne, rashin kiyaya ka'idoji ko kuma matakan kare kai.
Bayar da tazara da kuma sanya takunkumin hanci, na daga cikin ka'idojin da aka gindaya, misali a Jamus da sauran kasashen da suka ci gaba. Sai dai a kasashen Afirka, zai yi wahala abi ka'idojin musamman ma na bayar da tazara da gujewa cunkoso.