1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Dakarun Ukraine sun zafafa kai wa Rasha hare-hare

March 16, 2024

Sojojin Ukraine da mayaka masu ikirarin goyon bayan Kiev sun zafafa kai hare-haren a yankunan Rasha masu makwabtaka da kasar inda suka hallaka mutane a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4do2e
Dakarun Ukraine sun zafafa kai Rasha hare-hare
Dakarun Ukraine sun zafafa kai Rasha hare-hareHoto: Governor of Belgorod Region/REUTERS

Yayin da aka shiga kwana na biyu na zaben shugaban kasa a Rasha, dakarun Kiev sun zafafa kai hare-hare a yankunan Rasha masu iyaka da Ukraine inda suka halaka mutane biyu a baya-bayan nan, lamarin da kai shugaba Putin ga sha alwashin daukar fansa.

Harin karshe shine wanda aka kai a Belgorod birni mafi kusa da Ukraine inda aka cilla rokoki guda takwas, lamarin da ya ajalin wata mata da wani mutum tare kuma da jikkata wadansu mutanen biyu kamar yadda gwamnan yakin Viatcheslav Gladkov ya sanar a shafinsa na Telegram.

Sakamakon karuwar hare-haren gwamnan ya kuma sanar da daukar matakin rufe cibiyoyin kasuwanci na birnin da makarantun wasu gundumomi da ke yanki na tsawon kwanaki biyu.

Rahotanni da ke fitowa kuma daga sauran yankunan Rashar na cewa an kama mutane da dama a jiya Juma'a da laifin kawo cikas da zaben shugaban kasar da za a kamalla a gobe wanda zai bai wa shugaba Putin sabon wa'adin mulki na shekaru shida.