1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Yuganda na mara wa Sudan ta Kudu baya

January 16, 2014

A karon farko a hukumance ƙasar Yuganda ta tabbatar cewa dakarunta na taimaka wa dakarun SPLA a fafatawar da suke yi da na 'yan tawaye a Sudan ta kudu.

https://p.dw.com/p/1AsO1
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Yayin da ake ci-gaba da ɗauki ba dadi a Sudan ta Kudu tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye, ƙasar Yuganda ta tabbatar cewa dakarunta na marawa gwamnatin Sudan ta Kudu ɗin baya a yaƙin da take yi da 'yan tawayen. Wannan labarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a makwabciyar ƙasa Habasha, da nufin kawo ƙarshen rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Tattaunawar da ake yi a ƙasar ta Habasha wato Ethiopia na gudana ne ƙarƙashin jagorancin gamaiyar tattalin arzikin ƙasashen gabacin Afirka, wadda Yuganda ke zama memba mai muhimmanci a cikinta.

Dakarun ƙetare a gumurzun Sudan ta Kudu

Sai dai shugaban Yugandar Yoweri Museveni ya ce dakarunsa na taimaka wa ƙungiyar SPLA, tabbaci na farko a hukumance cewa dakarun ƙetare sun shiga cikin gumurzun.

Uganda Militär
Hoto: picture-alliance/Demotix /Hudson Apunyo

Shugaban ya ƙara da cewa sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu ƙarƙashin ƙungiyar SPLA da kuma dakarunsa sun yi wani ƙazamin faɗa da dakarun 'yan tawaye a wani wuri mai tazarar kilomita 90 daga birnin Juba, inda ya ce an samu salwantar rayuka da yawa.

A hira ta musamman da sashen Swahili na gidan rediyon DW, kakakin rundunar sojin Yuganda, Laftanan Kanal Paddy Ankunda ya ce ƙasarsa ta tsoma baki a rikicin na Sudan ta Kudu ne a wani mataki na kwantar da kurar rikicin da kuma ceto 'yan Yuganda da rikicin ya rutsa da su a wannan jaririyar kasa.

"Mun samu labarin cewa akwai 'yan Yuganda da suka makale a garin Bor wadanda yawansu ya kai 1800, kuma kawo yanzu gamaiyar ƙasa da ƙasa ta gaza kai ɗauki a garin. Saboda haka muna ci-gaba da ƙoƙarin ganin zaman lafiya da tsaro sun dawo a garin. Akwai wasu 'yan Yuganda a wasu sassan ƙasar ko da yake ba za mu iya kaiwa kowane gari ba, amma zamu yi iya ƙoƙarin ganin mun ceto su. Zamu ci gaba da wannan aiki na tabbatar da tsaro a Juba."

Kwanaki biyar bayan ɓarkewar rikicin a ranar 15 ga watan Disamba Yuganda ta girke dakarun a Sudan ta Kudu to sai dai kawo yanzu ba a san takamammen irin aikin da suke yi a ƙasar ba.

Karuwar yawan waɗanda rikicin ke rutsawa da su

Alƙalumma sun nuna cewa kimanin mutane 10,000 aka kashe sannan fararen hula 400,000 sun tsere daga gidajensu, tun bayan ɓarkewar rikicin tsakanin dakarun da ke biyayya da shugaban kasa Salva Kiir da wani kawance mai rauni na 'yan tawaye karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar.

Südsudan Flüchtlinge an der Grenze zu Uganda
Hoto: DW/S. Schlindwein

Fada Jacob Thelekkaedan na majami'ar Don Bosco Salesian a birnin Juba ke kula da wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallinsu sakamakon rikicin. Ya ce akwai cunkoson jama'a a kusan dukkan sansanonin da suka tsugunar da 'yan gudun hijira na cikin gida, halin kuma da ake ciki yana kara yin muni.

"Sun yi tafiya mai nesa wasu sun kwashe kwanaki a kan hanya. Sun galabaita, suna tsoro ka da a yi musu kisan gilla. Ko da yake a cikin sansanoni akwai matsaloli, amma sun gwammace da zama a nan saboda tsaron lafiyarsu."

A ranar Alhamis ƙungiyar Human Rights Watch ta ce wallafa rahoto da ke nuni da yawaitar keta hakkin ɗan Adam a Sudan ta Kudu sannan ta ce an aikata munanan laifuka a kan fararen hula saboda dalilai na kabilanci.

Daga ƙasa za a iyasauraron wannnan rahoto

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane