1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwa kan hana baki shiga Amirka

February 7, 2017

Lauyoyin gwamnati a Amirka sun shigar da kara don kare matsayin shugaba Donald Trump na haramtawa al'umomin kasashen musulmi shiga ko zama a Amirka

https://p.dw.com/p/2X55Z
USA Präsident Donald Trump
Hoto: picture-alliance/abaca/O. Olivier

Gwamnatin Amirka na cigaba da fafutuka wajen kare matsayinta kan hana jama'a daga wasu kasashe bakwai shiga kasar, matakin da a ranar Juma'ar da ta gabata wata babbar kotun birnin Washington ta ce ya sabawa doka. Lauyoyin da ke bukatar a dawo da matakin nan take sun kafa hujjar karar da suka shigar gaban kotun daukaka kara dake birnin San Francisco ne da cewar shugaba Donald Trump na da damar yin hakan bisa dalilai na tsaro.

Wannan karar dai na zuwa a dai dai lokacin da kotunan daukaka kara ke ganin yiwuwar dawo da umurnin shugaba Trump da za a saurari bangarorin a yau Talata. Sai dai wasu ruwayoyin na nuni da cewa da wuya bukatar lauyoyin ta iya sauya matakin kotun ta birnin Washington da ta aibanta matakin shugaban na Amirka.