1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban mutane sun warke daga coronavirus

April 6, 2020

Sama da mutum dubu 264 sun warke, bayan an tabbatar cewa sun kamu da cutar nan ta coronavirus mai sarke numfashin bil Adama, yayin da ta kashe wasu dubbai a duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3aY8a
Tübingen | Dr. Julia Martin Li und ein Medizinstudent auf dem Weg zur ambulanten Versorgung
Hoto: Imago Images/ULMER Pressebildagentur

Kamar dai yadda bayanan da Jami'ar John Hopkins da ke bin diddigin yaduwar cutar da ke Amirka suka nunar, ya zuwa wayewar garin Litinin, akwai mutum fiye da miliyan daya da dubu 200 da cutar ta kama a fadin duniya.

Jami'ar ta kuma ce kimanin mutum dubu 70 ne kuma cutar ta kashe a sassa daban-daban na duniyar, musamman ma a kasashen da annobar ta fi tsanani a cikinsu.

Kasashen da lamarin ya fi munanan a cikinsu dai su ne Amirka da Spain da Italiya, sai Jamus da Faransa sannan sai kasar China.

Haka ma akwai kasashen irin su Iran da Birtaniya da Turkiyya sai kuma Switzerland.