1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya sake barkewa a arewacin Mali

November 12, 2023

Sojojin Mali da mayakan tawayen kasar sun sake gwabzawa, inda ta kai ga hare-hare da manyan makamai daga bangaren dakarun gwamnatin Assimi Goïta.

https://p.dw.com/p/4YixJ
Mayakan gwamnatin kasar Mali
Mayakan gwamnatin kasar Mali Hoto: PHILIPPE DESMAZES/AFP

Fada ya sake barkewa a yau Lahadi tsakanin sojoji da 'yan tawaye a arewacin Mali, inda dukkanin bangarorin ke ikirarin samun galaba a gumurzun da aka tafka.

Tun a karshen makon jiya ne runudnar sojin kasar Mali ta yi ta nausawa ta yankin Kidal, kuma ta fada ta shafukan zumunta cewar ta yi nasarar fatattakar 'yan tawayen a hare-haren sama da kasa.

Tun bayan karbe iko da gwamnati a shekara ta 2020 dai, sojoji a Mali sun himmatu ne ga kokarin kwato yankunan kasar da 'yan tawaye ke sheke a ya a ciki.

Sai dai kuma 'yan tawayen daga nasu bangaren suna ikirarin yi wa dakarun Mali da sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner kawanya a wajen Kidal din.