1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Fafaroma ya bukaci sasanta rikicin Afghanistan

August 15, 2021

Shugaban darikar Katholika na duniya, Fafaroma Francis, ya yi kiran tattaunawar da za ta samar da masalaha a rikicin kasar Afghanistan domin ganin an samo mafita.

https://p.dw.com/p/3z157
Symbolbild I Papst Franziskus
Hoto: Stefano Spaziani/picture alliance

Fafaroma na wannan kira ne a daidai lokacin da mayakan Taliban ke shiga Kabul babban birnin Afgahnistan, inda a gefe guda Amirka ke kwashe jami'anta na diflomasiyya a kasar.

Mabiya addinin Kirista dai kalilan ne a Afghanistan, galibi 'yan kasashen waje da ke aikin jakadanci da kuma masu ayyukan jin kai.

Rahotanni daga Afghanistan na cewa ana tattaunawa tsakanin mayakan Taliban da gwamnatin kasar domin ganin yadda za a mika mulki ba tare da zubar da jini ba.

Shekaru 20 da suka gabata ne dai sojojin taron dangi karkashin jagorancin Amirka da kungiyar tsaro ta NATO, suka kifar da mulkin Taliban da ke rike da iko a tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.

Tuni ma Jamus ta snar da rufe ofishin jakadancinta dake birnin Kabul a wannan Lahadi.