SiyasaJamus
Faransa na kokarin wanke kanta a kan kisa a Nijar
December 20, 2021Talla
Hukumomin kasar Faransa, sun ce sun gudanar da cikakken bincike a kan abin da ya haddasa mutuwar wasu mutum uku yayin sintirin dakarun kasar a Jamhuriyar Nijar cikin watan jiya.
A ranar Juma'a ne dai aka ji Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar, ya yi kiran da a gudanar da bincike a kan mutuwar mutanen, lokacin da ayarin dakarun Faransa ke kan hanyarsu ta zuwa Mali.
Wani bore ne dai ya tashi wanda ya haddasa asarar rayukan mutanen uku, wadanda bayanai ke cewa sojojin Faransa ne suka yi harbi, wasu kuma ke dora wa sojojin Nijar.
Ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta ce sojojin kasar sun yi iya kokarin ganin sun yi abin da ya dace a lokacin yamutsin.
Ministar ta kuma ce ana ci gaba da tattaunawa a kan batun da mahukuntan Jamhuriyar Nijar.