Farautar 'yan Isra'ila a filin jirgin saman Dagestan
October 30, 2023Kafofin yada labarai na kasar Rasha sun ruwaito cewar jama'ar da suka hallara filin jirgin dauke da tutocin Falasdinu sun yi ta furta kalaman kyamar Yahudawa tare da yunkurin kutsawa cikin jirgin da ya taso daga Tel-Aviv babban birnin Isra'ila.
Karin bayani: Zanga-zangar adawa da hari a sibitin Gaza
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Rasha ta ce an rufe filin jirgin na wani dan lokacin tare da karkatar da saukar wasu jiragen zuwa wadansu filayen jirgin sama. To sai dai gwamnatin Dagestan mai al'umma galibi musulmi ta ce an shawo kan lamarin bayan da aka baza jami'an tsaro.
A daidai lokacin aukuwar lamarin, Isra'ila ta kira Rasha da ta bai wa 'yan kasarta kariya yayin da wasu kasashe ciki har da Amurka suka yi Allah wadai da zanga-zangar nuna kyamar Yahudawa.
Karin bayani: Yaki da kyamar Yahudawa
A baya bayan nan an kona wata cibiyar Yahudawa a birnin Nalchik da ke yankin Kabardino-Balkarie kamar yadda kamfanin dillacin labarai na RIA Novosti ya ruwaito.