Dangantaka tsakanin Rasha da EU
January 15, 2015Mogherini ta nunar da cewa kungiyar ta EU za ta iya shirya yadda za ta dawo da huldar diplomasiyya da kasuwanci da sauran al'amura da kasar Rasha bayan da dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu sakamakon rikicin Ukraine. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa yaga takardar da ke kunshe da batun tattaunawar da aka rabawa gwamnatocin kasashen kungiyar ta EU 28 gabanin taron ministocin harkokin kasashen ketare na kasashen da za a yi a ranar Litinin din makon gobe a Brussels, wadda ke nuni da cewar ta yiwu kungiyar ta amince da hada kai da kasar Rasha wajen magance matsalar kasashen Siriya da Iraq da Libiya da Iran da Koriya ta Arewa da ma batun annobar Cutar Ebola mai saurin kisa da kuma na Falasdinu.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman