1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Adama Barrow ya lashe zabe

December 2, 2016

Madugun 'yan adawar Gambiya Adama Barrow ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi inda ya kada shugaba mai ci Yahya Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 a kan gadon mulki.

https://p.dw.com/p/2TehK
Gambia Präsidentschaftswahl Adama Barrow
Hoto: Getty Images/AFP/STR

Sakamakon zaben shugaban kasar da aka fidda a zaben da aka yi a kasar Gambiya ya nuna cewar shugaban kasar Yahya Jammeh ya sha kaye a zaben inda madubun 'yan adawa Adama Barrow ya samu galaba da kashi 45 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da shugaban Jammeh ya samu kashi 36 cikin 100.

Shugaban hukumar zaben kasar ta Gambiya Alieu Momarr Njai ya ce kasancewar Mr. Barrow ya samu kuri'u mafi rinjaye, hukumar zaben kasar ta bayyana shi a matsayin wanda zai maye gurbi Shugaba Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 ya na mulkar kasar. Tuni ma dai shugaban na Gambiya Yahya Jammeh ya taya abokin karawarsa murnar lashe zaben kana ya yi na'am da irin sakamakon da aka fidda.