1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya: Zargin wawashe dukiyar gwamnati

January 23, 2017

Sabuwar gwamnatin Gambiya ta ce kasar na cikin yanayi na matsalar kudi, biyo bayan zargin da ta yi na cewar tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya yi awon gaba da wasu makudan kudade kafin ya bar kasar.

https://p.dw.com/p/2WGtv
Gambia Adama Barrow gewählter Präsident
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Bayan da kungiyar ECOWAS ta shiga tsakani a rikicin siyasar kasar Gambiya wanda hakan ya sanya tsohon shugaban kasar da ya sha kaye a zabe Yahya Jammeh ya bar gadon mulki har ma ya kai ga ficewa daga kasar, sabuwar gwamnatin kasar da Shugaba Adama Barrow ke jagoranta ta ce kasar fa ta fada wani wadi na rashin kudi sakamakon wawashe lalitar gwamnati da Jammeh ya yi kafin ya fice daga kasar a karshen makon da ya gabata. Gwamati ta Barrow dai na cewar kudaden da ake zargin Jammeh din ya kwashe sun tasamma dalar Amirka miliyan 11, sannan kuma ya tafi da wasu motoci na alfarma mallakin gwamnati.

Wani mashawarcin shugaba Adama Barrow Mai Ahmad Fatty ya shaida wa manema labarai a Dakar babban birnin kasar Senegal inda sabon shugaban na Gambiya yake a halin yanzu cewar: ''ta fuskar tattalin arziki, Gambiya na cikin garari, kusan ba komai a asusunta. Kwararru a ma'aikatar kudi da kuma babban bankin kasa ne suka tabbatar da hakan.''

Wani abu har wa yau da yake cigaba da jan hankalin sabuwar gwamnati da ke shirin kama aiki da ma 'yan kasar shi ne batun tsaro musamman ma dai a fadar shugaban kasa, sai dai wata majiya ta shaidawa DW cewar an ga wasu ma'aikata na fadar na shirye-shirye a wannan Litinin (23.01.2017) na kintsa fadar ta yanda Shugaba Adama Barrow zai shigo ba tare da ya fuskanci matsala ba. A bangare guda kuma ana sa ran dakaru 7000 na kasashe makwabatan da ke kasar a halin yanzu, za su ci gaba da zama har sai lamura sun dai-daita.