1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghetto Classics na karbuwa a Kenya

Kamaluddeen SaniNovember 4, 2015

Kada kayayyakin waka ga matasan nahiyar Afrika ba wani abu sabo ba ne to amma irin yadda matasan ke nuna shaukin wakoki irin su Brahms da Haendel abu ne mai ban mamaki.

https://p.dw.com/p/1GzQn
Ghetto Classics Nairobi
Mawakin Ghetto ClassicsHoto: Antje Passenheim/WDR

Dai-dai lokacin da mawakan zamanin da tauraruwarsu ke haskawa a duniya irin su Brahmas da Haendel su kuwa Matalautan kauyukan birnin Nairobin Kenya hatta yanayin wakokin nasu basu da masaniya da su ,to sai dai yanzu wani sabon shiri da aka bullo da shi mai suna Ghetto Classics ya fara kawo sauyi matuka ba wai ta bullo da sabbin wakoki ba har ma da nunawa matasa sama da dari 300 wata muhimmiyar damar kauce wa tafka manyan laifuffuka gami da yin adabo da shan miyagun kwayoyi.

Kada kayayyakin waka ga matasan nahiyar Afrika ba wani abu sabo ba ne to amma irin yadda matasan ke nuna shaukin wakoki irin su Brahms da Haendel abun e mai ban mamaki. abin mamakin ma shi ne yadda wakokin ke tasiri a tsakiyar wata unguwa mai suna Korogocho da ke wajen birnin Nairobi Kenya wanda shi ne abinda kungiyar Ghetto Classics suke yi.

Seline Akumu tana daya daga cikin 'yan kungiyar ita da suran 'yan kungiyar na iya sarrafa kowace waka zuwa kida irin na zamani.

Ghetto Classics Nairobi
Matasa da ke kidan Ghetto ClassicsHoto: Antje Passenheim/WDR

"Kade-kaden Ghetto Classics shi ne abu na biyu bayan dangina, dukkanin mu a nan tamkar 'yan uwa maza da mata ne don haka mai yuwa ne idan zaman gida ya gundire ni ko kuma ina son shakatawa sai kawai na taho nan".

Saline da 'yan kungiyarsu ta mawaka sun lalulo wata hanyar da za su samarwa kansu kima da daraja.

"Wani lokaci yadda mutane suke magana da kai zaka fahimta cewar daga wani yanayi na taluci ka futo,wannan yana bani takaici kuma wannan ne nake son canjawa".

Saline wacce ke koyar da darussan kade-kade na samun Euro har 45 a wata, wannan na nuni da cewar ta fara tsayawa da kafafunta to amma duk wadanan abubuwan ba za su faru ba in ba dan tallafin Elizabeth Njoroge ba wacce ta kirkiro da kungiyar Ghetto Classics.Elizabeth ta ce:

" Lokacin da muka fara an dauka shirme muke yi, ana cewar bata lokaci muke yi to amma duk da yadda ake kyamar wakokin a matsayin mu na mata, na tuna ranar da muka fara wakokinmu a nan sai gamu mun bulla tamkar mun fado daga sama".

Ghetto Classics Nairobi
Mawakin Ghetto Classics a NairobiHoto: Antje Passenheim/WDR

To amma sannu-sannu kwana nesa inji Hausawa jim kadan da samun tallafin kudade daga cibiyar raya al'adu da kade- kade ta kasar Kenya kungiyar tauraruwarta ta fara haskakawa.

"Bana jin dukkanin wadannan kanan yaran da ke karbar darusan wakokin za su yi fice to amma shakka babu yarinya irin su Seline tana da hazaka kwarai da gaske kuma bana jin dadi idan aka ce Seline ba ta samu damar halartar darussan mu ba a lokacin da take karama domin da mun yi arangama da ita a lokacin da take shekaru 8 ko 9 Allah ne kadai yasan abin da za ta zama a nan gaba.

Seline dai yanzu haka ta zama wata tauraruwa ga 'yan baya musamman wajen nuna kwazo da juriya gami da aiki tukuru ta hanyar Ghetto Classics da ke Krogocho.