Gobara ta halaka jama'a a Kenya
June 28, 2018Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Nairobi babban birnin kasar Kenya, na cewa wata gobara ta kashe akalla mutum 15 wasu da dama kuma sun jikkata a wata kasuwar da ke a birnin, kamar yadda wasu jami'an lafiya suka tabbatar a wannan Alhamis. Bayanai sun ce an kuma yi asarar dukiya mai yawa a ibtila'in, wanda ya faru da misalin karfe biyu na dare agogon kasar. An wallafa wasu hotunan irin ta'asar da gobarar ta haddasa.
Wata majiya ta St. Johns, wadda ke aikin kwashe wadanda abin ya shafa, ta ce an kwantar da wadanda suka jikkata su 70 a asibitin Kenyatta da ke a birnin na Nairobi.