Brazil: Ambaliyar ruwa ta yi sanadin gomman rayuka
May 4, 2024Talla
Hukumomi na cewa fiye da mutane 24,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon iftila'in ya shafi anguwanni fiye 265 a jihar Rio Grande do Sul. Shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana iftila'in ambaliyar ruwa ta wannan lokacin a matsayin mafi muni a tarihin kasar. An tura da jami'an agaji a fiye da 2,000 zuwa sassa daban-daban domin kai dauki ga jama'a. Kawo yanzu dai an ceto 8,000. Tun a ranar Litinin ce ake tafka ruwan sama wanda ya haifar da iftila'in da ya mamaye gidaje da lalata hanyoyi da kuma gadoji.