1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya gana da Lavrov kan Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
April 26, 2022

A ziyararsa ta farko a Moscow tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya roki bangarorin da ke fada da juna da su tsagaita wuta cikin hanzari a Ukraine.

https://p.dw.com/p/4AS7W
Russland Moskau UN Generealsekretär Antonio Guterres
Hoto: Maxim Shipenkov/REUTERS

 A lokacin tattaunawarsa da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, Mista Guterres ya ce ba abin da ke gabansu illa samar da yanayin tattaunawar tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Ukraine.

Bayan ganawarsa da Lavrov, Mista Guterres zai samu tarba daga shugaba Vladimir Putin na Rasha. Daga bisani kuma ya zai je kyiv babban birnin Ukraine, inda yake shan kakkausar suka daga shugaba Volodymyr Zelensky dangane tsarinsa na fara zuwa Rasha, lamarin da ya ce "babu adalci" a cikinsa.

Tun bayan kutsawar Rasha a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, Majalisar Dinkin Duniya ta zama saniyar ware a wannan rikici, sakamakaon rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe biyar masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhun, wanda Rasha ke cikin su.