1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nijar ta gargadi kamfanin ORANO

Issoufou Mamane
June 17, 2024

Ministan kula da ma'adanan Nijar ya bai wa kamfanin ORANO da ke aikin hakar ma'adanin Uranium a kasar wa'adi ya fara aiki ko a kwace soke lasisinsa

https://p.dw.com/p/4hALs
Kamfanin makamashi Uranium da ke Arilit
Kamfanin makamashi Uranium da ke ArilitHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Malam Aysemi Tchiroma na kungiyar nan ta ROTAB da ke sa ido ga ma'adanan kasar ya yi wa DW bitar abin da ya kai gwamnantin daukar wannan matakin.

"Tun lokacin shugaban kasa Tanja Mamadou aka fara wannan zancen na azo a fara aikin, shugaban kasa Tanja Mamadou ya basu umurnin cewa in basu yi wannan aiki ba zai kwace izinin da ya basu da suka yi kamar za su farawa, a nan kuma Allah da nashi iko shugaban kasa Tanja Mamadou ya bar iko, Mahamadou Issoufou ya zo suka yi ta kuma kewaye kewaye har dai aka zo lokaci' shugaban kasa Mohamed Bazoum shi ma a wannan lokacin ministan da ke kula da ma'adanan ta yi musu kashedi da su fara aiki basu yi ba. ''

Kamfanin makamashi Uranium da ke Arilit
Kamfanin makamashi Uranium da ke ArilitHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

To cikin yanayi na samarwa kasar 'yancinta bisa ga juyin yaya hali ga sabuwar tafiya da kasar ke yi sabbin hukumomin mulkin sojin Nijar suka dauki wannan matakin.

Kodayake ga Allassan Abubakar na kungiyar fafutukar ganin an raba gari da turawan jari hujja, TLP tournons la page yace wannan jan kafar da suke ta na da tushe 

" ina son in tuana wa mutane a 2012 akwai matasa na kasar Faransa ita wannan mahakar ta Imouraren ba za ayi amfani da ita ba sun dauka wannan guri ne wanda ya kamata a ajiye wa matasan kasar Faransa saboda wancan guri na comminak da aka dade ana amfani da shi tsawon shekara 40 sun dauka na muaten da suka gabata ne wadanda tsufa ya soma kamawa yanzu sun dauka na matasa ne suka nemi kasar Faransa ta jinkirta wannan abu dalillai wadanda suka fara fitowa azzahiri wanda kowa ya gane su ita ce wannan zanga zaganr da matasan Faransa suka yi yana ciki. Wannan shi ne abunda ya kamata mutane su yi amfani da shi a kai "

Kamfanin makamashi Uranium da ke Arilit
Kamfanin makamashi Uranium da ke ArilitHoto: Issouf Sanogo/AFP/picture alliance/dpa

To sai dai ga Kadi Mani Basiru na kungiyar kwadago ta USES/NIGER, jinkirin aikin ko ma sabuwar dabara daga kamfanin na ORANO ba zai hana 'yan kasar su raba gari da turawan Faransa ba:

A cikin wannan yanayi ne da dama daga cikin 'yan Nijar na alakanta matakin da sabuwar huldar da kasar ta kulla da Rasha da ma Iran akan batun makamashin.