1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tigray ya koma hannun gwamnatin Habasha

December 4, 2020

Lamura sun fara dawowa kamar yadda suke a baya a Tigray da ke arewacin Habasha, bayan shafe tsawon wata guda ana fafatwa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen yankin.

https://p.dw.com/p/3mF3n
Äthiopien Abiy Ahmed
Firaminstan Habasha Abiy AhmedHoto: Amanuel Sileshi/AFP

Yanzu haka dai mutane kusan dubu 50 ne 'yan Habasha ke gudun hijira a makwabciyara Sudan. Sai dai duk da dimbin 'yan kasar ta Habasha da ke gudun hijira a gabashin Sudan din, wani gidan talabijin na Habashan  ya nuna manyan titunan Makelle babban birnin yankin Tigray, inda babu kowa sai sojojin kasar kawai ke shawagi, wata alama da ke nuna cewa ikon yankin ya dawo hannun gwamnatin Habasha.

Karin Bayani: 'Yan Habasha na tserewa zuwa Sudan.

Atikilt Kiros wani mazaunin birnin Makelle ya bayyana cewa harkokin kasuwanci sun fara dawowa birnin, inda masu shaguna suka fara budewa bayan shafe wata daya suna kulle, yayin da ake dauki ba dadi tsakanin 'yan awaren yankin da sojojin gwamnatin kasar ta Habasha: ''Kamar yadda idanunku suke gane maku mutane sun fara komawa harkoki, zaman lafiya ya soma samuwa tunda har shaguna sun bude, kuma za mu ci gaba da zuwa coci nan ba da jimawa ba.''
Gwamnatin ta Habasha dai ta yi fatan ganin kwarya-kwaryar zaman lafiyar da aka samu zai zama darasi ga duniya cewa illahirin ikon kasar ya koma hannun gwamnati, ba kamar yadda mayakan Tigray ke ikirarin iko da yankin ba. Wani abin da ake ganin ka iya yin zagon kasa ga zaman lafiyar da aka fara samu shi ne, ikirarin da madugun 'yan awaren ya yi na ci gaba da gwabza fada duk da nasarar da Firaminista Abiy Ahmed yake tunkahon samu.

Äthiopier Flüchten vor Kämpfen in Tigray in den Sudan
Dubban 'yan Habasha sun tsere zuwa makwabciyatra Sudan domin gujewa rikiciHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Karin Bayani: Rikicin 'yan aware ya ta'azzara a Afirka

A birnin na Makelle sojojin Habasha sun bankado wani katafaren runbun ajiye makamai makare da kayan yaki, kamar yadda babban kwamandan rundunar sojojin gwamnati da ke yaki da 'yan awaren Sadik Ahmed ya yi karin haske: ''Muna ci gaba da yin bincike dangane da makaman tun da hukuma ba ta san da su ba. Haka kuma cikin 'yan kwanakin nan mazauna yankunan suna ta mika makamansu ga hukuma, kai har da matan aure ma da mazajensu suka gudu suna nuna mana inda mazajen suka adana makamai.''

Rikicin  da ya dauko hanyar tabarbara lamura a kasar da ma daukacin yankin kahon Afirka, ya samu dauki daga Majalisar Dinkin Duniya bayan da ta shiga wata yarjejeniya da gwamnatin Habasha da nufin samun damar kai agaji a wuraren da gwamnati ke da cikakken iko. Kawo yanzu dai hanyoyin sadarwa da na sufuri duk a toshe suke a yankin na Tigray.