1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka tana kara samun matsalolin 'yan aware

Uta Steinwehr LMJ
November 24, 2020

Rikicin 'yan aware na kara fadada a nahiyar Afirka. Na baya-bayan nan da ke ci gaba da ta'azzara, shi ne na 'yan awaren Tigray da ke kasar Habasha. Wannan na zaman misali ne kawai.

https://p.dw.com/p/3lknY
Präsidentschaftswahl in Kamerun Sicherheitskräfte
Hoto: DW/F. Muvunyi

Yawancin wadannan rigingimu, sun samo asali ne daga lokacin Turawan mulkin mallaka. Kama daga 'yan awaren Ambazoniya a Kamaru zuwa ga 'yan Togoland a Ghana da 'yan Biafra a Najeriya da Zanzibar a Tanzaniya da kuma Cabinda a Angola, duk wadannan na ikirari na 'yancin kai da kuma barazanar ballewa daga aininhin kasashen da suke ciki a yanzu.  Rikici ya tilasta 'yan Habasha gudun hijira


Masana dai na ganin cewa, a duk lokacin da aka samu matsalar 'yan aware a kasa, tattalin arzikin kasar na taka muhimmiyar rawa a rikicin.Sai dai duk da cewa Farfesa Toyin Falola malamin tarihi a jami'ar Texas da ke Amirka da kuma Lotje de Vries mataimakiyar farfesa a jami'ar Wageningen ta kasar Netherlands sun amince da batun rawar da tattalin arzikin ke takawa, dukkansu suna da ra'ayin cewa, maatsalolin sun samo asali ne tun lokacin mulkin mallaka. Farfesa Toyin Falola na da ra'ayin cewa tun lokacin da Turawan mulkin mallaka suka yi watandar nahiyar Afirka tsaknin su yayin taron Berlin shekarun 1884 da 1885, bayan  kammala yakin duniya na daya aka samar da wannan matsala.

Bayan kammala yakin duniya na daya, an mika Kamaru da a baya ke karkashin mulkin mallakar kasar Jamus zuwa ga kasashen Faransa da Birtaniya. A shekara ta 1961 an yi kuri'ar raba gardama domin samar da yankin Kamaru ta Birtaniya, inda yankin arewacin Kamaru zai ksance karkashin Najeriya kana kudanci ya kance Jamhuriyar Kamaru bangaren Faransa. A yanzu bangaren da ke magana da harshen Turancin Ingilai sun kasance maraa rinjaye, kuma suna jin tamkar ba su da muhimmanci kamar 'yaan uwansu masu magana da harshen Faransaci. Rikicin na yankin Ambazoniya da aka kwashe shekaru uku ana fama da shi, ya halaka sama da mutane 3000 kawo yanzu.   Kamaru: Gwamanti ta samar da zaman lafiya

Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba


Suma dai 'yan awaren Togoland na kasar Ghana suna kamanceciniya da na Ambazoniyar Kamaru, bayan kammala yakin duniya na daya ne aka rabawa Faransa da Birtaniya kasar Togo da ita ma a baya ke karkashin mulkin mallakar Jamus. Bangaren Yamma da ya fada hannun Birtaniya, a yanzu yana cikin Ghana, yayin da bangaren Gabas da aka bai wa Faransa ya kasance Togo. A karshen watan Satumbar wannan shekara, 'yan awaren gabashin Ghana, sun mike domin neman 'yancin kai daga Ghana.   Ghana: 'Yan aware sun kai hari kan motocin sufuri mallakin gwamnati 

Ghana Volta Region
Hoto: Elvis Washington


Matsalolin addini ko kabilanci, rikicin Ambazoniya a Kamaru da na Togoland a Ghana ba sa rasa nasaba da rabon gadon kasashen Afirka da Turawan suka yi. A ta bakin Lotje de Vries mataimakiyar farfesa a jami'ar Wageningen ta kasar Netherlands, A mafi yawan lokuta ba a iya fahimtar dalilan da ke haifar da wadannan matsaloli, yana kuma da matukar wahala a iya gane wanne yanki ne ke zaman mallakin wannan kasa, misali idan aka yi la'akari da Zanzibar a Tanzaniya da kuma Cabinda a Angola.   Sojin Kamaru sun halaka 'yan aware da dama


A  Zanzibar ga misali, matsalar rashin shugabanci na gari ma na taka rawa, bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka na bayar da 'yancin kaia da kuma sanya su cikin mulki da sauran al'amuran da suka shafi kasa. De Vries na daga cikin eiditocin da suka yi gyar a littafin "Secession in African Politics" kuma ta ce ta fuskanci kalubale dangane da 'yan awaren Afirkan musamman ta fuskacin yadda suke bunkasa.


Sai kuma Biafra a Najeriya. Wani rikicin a Afirka ya barke ne bayan samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar. Misali rikicin 'yan rajin kafa kasar Biafra a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Shekaru kalilan bayan samun 'yancin kan kasar, aka fara gwabza yakin basasa tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970. A wannan lokacin, kimanin mutane dubu 500 zuwa miliyan uku ne suka halaka. A cewar masanin tarihi Falola wannan rikicin ya barke ne sakamkon rashain shugabanci na gari.

A cewar Farfesa Falola dalilin da ya sanya matsalolin da suka assasa rikicin Biafra a Najeriya a shekarun 1960, suka sake dawowa a yanzu, shi ne tun da fari ba a magance su ba.

Nigeria Kriegsmuseum Umuahia
Hoto: DW/K. Gänsler