1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Hare-hare kan motocin dakon kaya

Gazali Abdou Tasawa LM
December 19, 2024

Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da harin 'yan ta'adda a kan ayarin motocin dakon kayan abinci da kayan masarufi da suka taso daga tashar ruwan Lome ta kasar Togo zuwa gida.

https://p.dw.com/p/4oNdr
Nijar | Kan Iyaka | Benin | Malanville | Motocin Dakon Kaya
Manyan motocin dakon kaya, jibge a kan iyakar Nijar da BeninHoto: AFP/Getty Images

Hukumomin tsaron na Jamhuriyar Nijar sun ce lamarin ya wakana ne a cikin kasar Burkina Faso, inda 'yan ta'addan suka kona wasu tireloli dauke da hajoji. Tuni kungiyoyin direbobi da na 'yan kasuwar Nijar din suka soma nuna damuwarsu kan yadda mahukuntan Burkina Faso ke nuna gazawa wajen bayar da kariya ga motocin, lokacin da suka ratso kasarsu. Sai dai a cewar hukumomin an yi sa a ba a yi asarar rai ba, sai dai ta dukiya. Wannan dai ba shi ne karo na farko da 'yan ta'addan ke kaddamar da hari a kan ayarin motocin jigilar hajojin 'yan Nijar a wannan hanyar ba, lamarin da Malam Adamou Batchiri shugaban kungiyar 'yan kasuwar Albasa ta gunduma ta biyar a birnin Yamai ya ce na zama  daya daga cikin dalilin tsadar kayan masarufi da ake fama da su a yanzu haka a kasar. To amma daga nashi bangare Malam Soule Oumarou na kungiyar FCR nuna damuwa ya yi, kan yadda ya ce kasashen AES na kasa bayar da kariya ga motocin dakon kayan zuwa Nijar. Wannan hari na zuwa ne a daidai loakcin da kungiyoyin 'yan kasuwa da sauran 'yan Nijar ke ta kiraye-kiraye ga gwamnatin Abdourahamane Tchiani ta bude iyakar kasar da Benin, domin a koma shigar da kaya ta wanann hanya da nufin kawo karshen asarar rayuka da ta dukiya da Nijar ke yi a kan hanyar ta Burkina Faso.