1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya gana da Shugaba Joe Biden a Amurka

July 26, 2024

A ziyarar da ya kai kasar Amurka, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gana da Shugaba Joe Biden a fadar White House a ranarAlhamis.

https://p.dw.com/p/4iknR
Netanyahu da Biden a fadar White House
Netanyahu da Biden a fadar White HouseHoto: Susan Walsh/AP Photo/picture alliance

Yayin ganawar tasu dai, firaministan na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gode wa Shugaba Biden da abin da ya bayyana da taimako na shekaru 50 da Amurka ke bai wa kasarsa.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Mr. Netanyahu ya bayyana a gaban majalisar dokokin kasar ta Amurka.

Yayin da shugabannin biyu ke ganawa a jiyan, fadar White House ta nuna bukatar a tsagaita wuta a Zirin Gaza.

Firaminista Netanyahu dai na fuskantar suka daga iyalan wadanda kungiyar Hamas ke rike da su, saboda lokacin da aka dauka ba tare da an sasanta ba.

Hakan nan ma Isra'ilar na shan suka daga kasashen duniya dangane da hare-haren da take kaiwa a Zirin Gaza yau watanni tara ke nan.