1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin 'yan bindiga a Burkina Faso ya halaka mutane da dama

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 26, 2024

Wani jami'in tsaron kasar ya ce maharan sun dirar wa wani masallaci lokacin da ake sallar asuba a Lahadin nan, sannan suka bude wa masallatan wuta suka kashe su har da limaminsu

https://p.dw.com/p/4cttv
Hoto: Assane Ouedraogo/EPA-EFE

Wani harin ta'addanci a masallaci da coci a kasar Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da har yanzu ba a san adadinsu ba, kamar yadda kamfanin dillancin Faransa AFP ya rawaito.

Karin bayani:Burkina Faso: Dakile yunkurin tada zaune tsaye

Wani jami'in tsaron kasar ya ce maharan sun dirar wa wani masallaci lokacin da ake sallar asuba a Lahadin nan, sannan suka bude wa masallatan wuta suka kashe su har da limaminsu.

Karin bayani:Mali da Burkina Faso da Niger sun lashi takobin karfafa hulda

Yayin da kuma dai a Lahadin 'yan bindigar suka far wa wata mujami'a tare da kashe masu bauta 15 sannan suka raunata mutane biyu.