Hotunan waiwayen wasu abubuwa da suka faru a shekarar 2024 da ke ban kwana
Yakin Ukraine da Gabas ta Tsakiya, tare da zaben shugaban kasa a Amurka, na daga cikin manyan al'amuran da suka wakana a 2024.
Goyon baya ga dimukuradiyya tsantsa
Domin nuna jin kai da karbar mutane cikin aminci da dimukuradiyya, tare da yaki da masu nuna wariyar launin fata: Dubban Jamusawa sun hallara a birnin Hamburg a cikin watan Janairu don bayyana adawarsu a fili ga jam'iyya mai kyamar baki ta AfD. Kimanin mutane dubu 50,000 suka yi cincirundo, bayan da AfD ta fara yunkurin gabatar da tsarin korar duk wani mai tushen da na Jamusawa ba.
Matsalolin jin kai da ake fuskanta dalilin yakin Sudan
Sama da shekara guda kenan da barkewar yakin basasa a Sudan. Rikicin ya samo asali ne a tsakiyar watan Afiriliun 2023 a dalilin neman kwatar ikon kasar tsakanin sojoji da dakarun RSF. Lamarin da ya raba mutane sama da miliyan 14 da gidajensu. Sama miliyan 25 suka fada cikin kangin annobar yunwa. Har ma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shi a matsayin yanayi mafi muni a duniya.
Ban kwana ga fatan samun kyautatuwar Rasha
Alexei Navalny mai shekaru 47, ya yi kaurin suna wajen sukar lamirin fadar Kremlin. Ya mutu a ranar 19 ga Janairu, cikin yanayi mai sarkakiya a kurkukun Rasha. Ya yi fice wajen yaki da cin hanci da rashawa da ya zargi gwamnatin Rasha da aikatawa, dalilin yanke masa hukuncin daurin shekaru 19 kenan. An binne shi a Moscow ba tare da gudanar da binciken gawarsa ba don gano musabbabin mutuwarsa.
Yadda 'yan Isra'ila ke zanga-zangar hana kai agaji jinkai ga Falasdinawan Gaza da ke fama da yunwa
Tabarbarewar halin jin kai a Gaza ya zama babban bala'i. Isra'ila ta dakile shigar da isassun kayan tallafin abinci ga al'ummar Gaza, wadda ke fuskantar annobar yunwa, kashi 90 cikin 100 na mutane miliyan 2 da fama da karancin abinci mai gina jiki. A cikin watan Fabarairu da kuma Mayu 'yan Isra'ila masu zanga-zanga suka tare manyan motocin dakon abinci a kai iyakar kasar don hana su shiga Gaza.
Zaman makoki a Rasha
Hari mafi muni da Rasha ta fuskanta a cikin shekaru 20, wanda ya yi sanadiyyar halaka mutane sama da 140, yayin da 360 suka jikkata, lokacin da aka kai hari wani gidan rawa a yankin Krasnogorsk na birnin Moscow. Kungiyar ta'addanci ta IS ce ta yi ikirarin kai harin. An kama mutane da dama da ake zargi da hannu a harin, kuma suke fuskantar shari'a.
Murnar amincewa da dokar shan tabar wiwi a Jamus
A ranar 1 ga Afirilu gwamnatin Jamus ta sahale amfani da tabar wiwi da bata wuce gram 25 ba, tare da amincewa mutane su yi nomanta a gida. Amma ba a amince a sha ta sasakai a cikin jama'a, sai an bada tazarar mita 200 ga makrantu da cibiyoyin kula da kananann yara, da wuraren wasanni da dai makamantansu.
Mawallafin shafin WikiLeaks Julian Assange ya shaki iskar 'yanci
Bayan shafe shekaru ana yi masa shari'a da kuma shekaru 5 a hannun Burtaniya, mawallafin shafin WikiLeaks Julian Assange ya koma Australia a cikin watan Yuni. Mr Assange ya kwarmata bayanan sirrin ta'annatin da sojojin Amurka suka aikata a Iraqi da Afghaninstan. Laifin da ya sa yake fuskantar hukuncin daurin shakru 175 a kurkuku. Amma aka cimma masalahar sakinsa da hukumomin shari'ar Amurka.
Yakin Ukraine da Rasha
A ranar 8 ga Yulin 2024, Ukraine ta fuskanci daya daga cikin munanan hare-haren da Rasha ta kai mata, tun bayan fara yakinsu a a cikin watan Fabarairun shekarar 2022. Mutane da dama ne suka halaka, bayan hari kan asibitin yara na birnin Kyiv. Kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar ta nuna cewa yakin ya halaka mutane 12,340 zuwa karshen watan Nuwamban 2024, cikinsu har da kananan yara 667.
Yadda aka yi yunkurin kashe Donald Trump
A ranar 13 ga Yulin 2024 tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya tsallake rijiya da baya, sakamakon yunkurin kashe da wani 'dan bindiga ya yi, lokacin da yake tsaka da jawabi a taron yakin neman zabe a Pennsylvania. Wani matashi ne mai shekaru 20 ya harbi Trump a kunne, aka garzaya da shi asibiti, sannan daga bisani aka sallame shi.
Yadda Isra'ilawa ke jimamin tunanawa da harin da kungiyar Hamas ta kai musu.
A ranar 7 ga Oktoba aka cika shekara guda da harin da Hamas ta kai Isra'ila, wanda ya kashe mutane kusan 1,200 tare da garkuwa da wasu 250. 'Yan uwa da abokan arziki sun yi jimamin wadanda aka kashe da wadanda aka yi garkuwa da su. An gudanar da zanga-zangar neman sakin kusan 100 da ke hannun Hamas . Kuma Isra'ilawa sun zargi Firaminista Benjamin Netanyahu da gaza yin katabus domin ceto su.
Isra'ila ta kashe jagoran kungiyar Hamas Yahya Sinwar
Isra'ila na daukar Yahya Sinwar a matsayin wanda ya kitsa kai harin ranar 7 ga watan Oktoba, wanda kuma ta kashe a Gaza bayan shekara guda da shirya wancan hari. Hoton da jirgi marar matuki ya dauko ne ya nuna shi kafin mutuwarsa. Kuma a cikin watan Agusta aka nada shi a matsayin sabon shugaban kungiyar, biyo bayan mutuwar shugabanta Ismail Haniyeh, da shi na Isra'ila ta halaka a birnin Tehran.
Gisèle Pelicot, matar da ta yi faftukar shari'a da wadanda suka yi mata fyade mai yawa a Faransa
Gisèle Pelicot ta zama abar misali cikin gwagwarmayar kare hakin mata. Shekaru da dama da suka gabata mai gidanta ya rinka gayyatar mutane ta intanret suna yi mata fyade bayan bata kayoyi masu bugarwa. Shi da mutane 50 ne suka fuskanci shari'a kuma kotu ta same su da laifi. Gisèle Pelicot ta ce makasudin tsayin dakan da ta yi a kan batun shi ne don yaki da cin zarafin mata a Faransa da ma duniya.
Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasa a Amurka
A ranar 5 ga watan Nuwamba Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasa a Amurka bayan samun nasara jihohi masu tasiri irin su Pennsylvania da Wisconsin da Georgia da kuma North Carolina. Masu sa ido kan zaben daga kasashen waje na nuna damuwar tasirin dawowar Trump kan karagar mulkin Amurka a karo na biyu, a kan yakin Ukraine da rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma yaki da dumamar yanayi.
Rushewar gwamnatin hadaka ta Jamus
A cikin watan Nuwamba ne gwamnatin hadaka ta jam'iyyun SPD, da Greens da FDP ta rushe, bayan da shugaban gwamnatin Jamus na jam'iyyar SPD Olaf Scholz ya kori ministan kudi Christian Lindner, bisa zargin karya ka'idar aiki. A ranar 16 ga Disamba majalisar dokoki ta Bundestag ta kada kuri'ar yankan kauna ga gwamnatin Scholz. Inda za a gudanar da zabe a ranar 23 ga Fabarairun sabuwar shekarar 2025.
Karshen mulkin Bashar Assad na Syria
Al'ummar Syria da ma 'yan siyasa da sauran mutane a sassan duniya na nuna murna da ganin karshen mulkin Bashar al-Assad. A cikin kwanaki 10 'yan tawayen HTS suka hambarar da gwamnatin Baath da ta shafe shekaru 61. Kimanin mutane 600,000 ne suka rasa rayukansu a karkashin mulkin danniya na Bashar Assad. Dubbai daga ciki an azabtar da su a ne kurkuku har suka mutu.
Isra'ila na fuskantar tuhuma a kotunan duniya
A cikin watan Janairu ne Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya ta ICJ. A cikin watan Nuwamba kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bada umarnin kama firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant. Isra'ila ta musanta aikata laifin. Mutane 45,000 Isra'ila ta halaka a Gaza, amma wasu sun ce adadin ya wuce haka.