1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

ICC ta ce toshe agajin Gaza laifin yaki ne

October 30, 2023

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta bayyana matakin Isra'ila na toshe kai kayan agaji zirin Gaza a matsayin laifin yaki.

https://p.dw.com/p/4YBQ4
ICC ta ce toshe hanyar kai agaji Gaza laifin yaki neHoto: AFP

Yayin da da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a Gaza tsakanin kungiyar Hamas da dakarun Isra'ila da suka kutsa zirin ta kasa, kotun kasa-kasa ta ICC ta bayyana matakin Isra'ila na toshe kofofin shigar da kayan agaji yankin a matsayin babban laifin yaki.

Karin bayani:Kungiyoyin agaji na kiran da a kawo karshen luguden wuta a Zirin Gaza

Babban mai shigar da kara na kotun mai hukunta manyan laifuka Karim Khan ne ya bayyana hakan a daidai lokacin da ya ziyarci garin Rafah da ke kan iyakar Masar da zirin Gaza inda kayan agaji ke jibge sabili da hana damar isar da su.

Karin bayani:  An katse hanyoyin sadarwa da lantarki a Gaza

Karim Khan ya kuma kara da cewa dole ne Isra'ila ta tabbatar da cewa wannan tallafin na kayan abinci da magunguna sun isa hannun fararen hula da ke cikin garari a zirin Gaza sakamakon rikicin da aka kwashe sama da makonni uku ana gwabzawa tsakanin dakarun kasar da kungiyar Hamas.