1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran na da sinadarin nukiliya mai yawa

Mahmud Yaya Azare LMJ
June 1, 2022

Wani sabon rahoto da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA ta wallafa, ya yi ikirarin bankado wasu boyayyun cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliya masu yawa a Iran.

https://p.dw.com/p/4C9hm
IAEA I Darakta I Rafael Mariano Grossi
Daraktan hukumar IAEA Rafael Mariano GrossiHoto: Lisa Leutner/AP Photo/picture alliance

Rahoton na IAEA dai, ya sanya hantar wasu kasashe a Gabas ta Tsakiya ta kada. Rahoton ya ce zuwa ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata bayan kwashe watanni 18 Iran tana wasa da hankalin hukumar da yi mata dungu, a yanzu ta bankado cewa yawan sinadarin Uranium da Iran ta samu ya rubanya fiye da sau 18 a kan wanda aka amince da shi a yarjejeniyar da Iran ta cimma a shekarar 2015 da a hukumance ake kira "Joint Comprehensive" ko kuma (JCPOA). Hukumar ta ce a yanzu haka, jimillar sanadarin nukiliyar da Iran din ta samu ya haura kilogiram 3,500. A cewar hukumar. Adadin ya kai matakin kaso 90 bisa 100 da zai iya ba ta damar kera makamin nukiliya, kamar yadda shugaban hukumar Rafael Mariano Grossi ya nunar. Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran din ta bakin kakakinta Saeed Khatibzadeh ta caccaki wannan rahoton, inda ya siffanta shi da na neman mayar da hanun agogo baya a yunkurin da ake na cimma sabuwar yarjejeniyar nukiliya da kasashen duniya.

Iran | Makamin Roka I Noor-2
Iran ta yi gwajin makami mai linzami, a cikin watan Maris din wannan shekaraHoto: Iranian state television/AP/picture alliance

A cikin watan Maris din wannan shekarar ne dai, Iran din da hukumar ta IAEA suka amince da salon da za a yi amfani da shi wajen warware matsalolin da ke tattare da cibiyoyin nukiliyar ta bayan da Tehran ta gabatar da bayanai ga hukumar tare da amsoshi a rubuce kan tambayoyin da IAEA din ta gabatar a kan wannan batu. Tuni dai kasar Isra'ila wacce a makon da ya gabata ita ma ta yi ikirarin bankado wasu boyayyun cibiyoyin sarrafa nukiliya a kasar ta Iran, ta siffanta rahoton da wata kwakkwarar hujja da ke tabbatar da rashin amfanin tattaunawa da  Tehran har ma ace za a cimma wata yarjejeniya da ita tana mai shan alwashin daukar duk matakan da suka wajaba ciki har da kai hare-haren rokoki domin ganin Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. A yayin da ita ma Saudiya ta bakin ministan harkokin wajenta Faisal bin Farhan Al Saud ta nuna kaduwarta da rahoton, tana mai kira da a sake matsa kaimi wajen takawa kasar ta Iran birki domin ganin ba ta dauki matakin da ya ce zai jawo gasar mallakar makamin nukiliya a Gabas ta Tsakiya.