1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
IlimiKamaru

Kamaru: Yajin aikin malaman jami'a

Zakari Sadou LM
January 9, 2025

Kungiyar malaman gaba da sakandare a Kamaru ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, wanda ta fara ranar takwas ga wannan wata na Janairu har sai gwamnati ta biya alawus din da suke binta tsawon shekaru.

https://p.dw.com/p/4ozfK
Kamaru | Shugaban Kasa | Paul Biya
Shugaban kasar KAmaru Paul BiyaHoto: Jacovides Dominique/Pool/ABACA/picture alliance

Sakamakon yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'in Kamarun ta SYNES ta shiga dai, an samu taruwar jama'a a kusa da jami'o'in da kuma gine-ginen gwamnati musamman a birane kamar Yaounde. Babban abin da kungiyar malaman manyan makarantun gwamnatin ke nema a Kamaru shi ne, biyan alawus din da aka bayar tun daga shekara ta 2009. Duk da cewa wadannan bukatu da malaman makarantun ke nema hakkinsu ne ba bara suke yi ba, sun jima suna nema a biya su bashin da suke bin gwamnati musamman sashen ilimin likita da bincike da sune ya cancanci a sanya a sahun gaba wajen biya musu bukatunsu wanda ya kama kimanin CFA miliyan 300.

Kamaru | Yajin Aiki | Malamai | Jami'o'i
Sashen koyon aikin likita, na daga cikin bangarorin da ke kokawa da rashin alawusHoto: Brent Stirton/Getty Images

Shugaba a ofishin ma'aikatar ilimi mai zurfi da ke kula da wadannan kudi Paul Henri Nguele-Nguele ya amince da wasu jinkirin da aka samu, sai dai a ganinsa malaman na amfani da wata damar da suke da ita na yin barazanar shiga zanga-zanga da ya ce hakan ba daidai ba ne. Idan har daliban kasar suka goyi bayan wannan yajin aikin, akwai yiwuwar barkewar zanga-zangar da za ta iya haifar da arangama da jami'na tsaro abin da ba bukata a wannan lokaci da ake ta kai ruwa rana tsakanin gwamnatin kasar da da wasu kungiyoyin fararen hula.

Hari kan yara 'yan makaranta a Kamaru

An tsaurara matakan tsaro da kuma takaita zirga-zirgar ababen hawa, musamman a kusa da wuraren da ake fargabar barkewar zanga-zanga. A shekara ta 2023 ne malaman makarantun sakandare na gwamnati suka tsunduma yajin aiki mai Taken "On a trop supporter," wato "mun jima muna hakuri." Sun dai bukaci a biya su albashinsu da suke bin gwamnatin kasar na tsawon shekaru da dama ne, inda kawo yanzu da yawa daga cikin malaman ba su samu kudin ba. Hakan dai ya tilasata da yawansu sun tsere zuwa kasashen ketare, domin samun ingantacciyar rayuwa duba da matsin da suke fuskanta.