1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Isra'ila ta ce ta gurgunta kungiyar Hamas

January 7, 2024

Dakarun Isra'ila sun ce sun karya kungiyar Hamas a yankin Zirin Gaza. Wannan na zuwa yayin da ma'aikatar lafiya a yankin Falasdinu ke bayyana mutanen da suka mutu a yakin.

https://p.dw.com/p/4aw9R
Dakarun Isra'ila da ke kai farmaki a Gaza
Dakarun Isra'ila da ke kai farmaki a GazaHoto: Israel Defense Forces/Handout via Xinhua/picture alliance

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta yi nasarar gurgunta kungiyar Hamas a yankin arewacin Zirin Gaza, a ci gaba da yaki da ke faruwa tsakanin bangarorin biyu.

Mai magana da yawun runduanra mayakan na Isra'ila, Daniel Hagari ya ce sun yi nasarar kashe kimanin 'yan kungiyar Hamas 8,000 a raewacin Zirin.

A gefe guda kuwa ma'aikatar lafiya da ke karkashin Hamas a Gazar, ta ce hare-haren da Isra'ila ke kaddamarwa sun kashe mutum dubu 22 da 722 tun lokacin da Isra'ila ta fara bude wuta.

Ma'aikatar dai ba ta fayyace adadin fararen hula da kuma mayaka daga cikin wannan adadi ba.

Isra'ila dai na musanta adadin, amma kuma Majalisar Dinkin Duniya da ma wasu kungiyoyi masu sa ido, sun ce tabbas wannan adadi gaskiya ne babu wani kwange a cikin sa.