1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila ta kashe kwamandan Hamas da ya kai harin makon jiya

October 14, 2023

Adadin wadanda suka mutu daga hare-haren Isra'ila a Gaza ya zarta mutum 2,200, yayin da wasu sama da 8,000 suka jikkata a daidai lokacin da aka kashe kwamandan Hamas.

https://p.dw.com/p/4XXNo
Hoto: Yasser Qudih/AFP/Getty Images

Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta tabbatar da kashe kwamandan kungiyar Hamas Ali Qadhi, wanda shi ne ya jagoranci harin kan iyaka da aka kai kan gidajen 'yan Isra'ilar a ranar Asabar ta makon jiya.

Sojojin na Isra'ila sun kuma ce an kashe Ali Qadhi, yayin wani hari da jirgi maras matuki, bayan samun bayanan sirri.

A wani labarin kuma kungiyar Hamas ta ce hare-haren da Isra’ila ke kai wa cikin sa’o’i 24 da suka gabata, sun yi ajalin mutane tara daga cikin wadanda ta ke garkuwa da su a yankin.

Sojojin Isra'ila sun tabbatar da gano gawarwakin wasu 'yan kasar da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su bayan harin da ta kai a ranar Asabar.

Sojojin na Isra’ila sun gano gawarwakin ne a lokacin wani samame ta kasa da suka kai yankin na Gaza.