1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta sha alwashin yin fito-na-fito da Iran

August 2, 2024

Isra'ila ta sha alwashin cewa, ba za ta da nade hannu ba idan har Iran ta kaddamar mata da hari a matsayin ramuwar gayya kan kisan shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh.

https://p.dw.com/p/4j3eH
Jana'izar shugaban Hamas, Ismail Haniyeh a Katar
Hoto: Uncredited/Qatar TV/AP/dpa/picture alliance

A zantarwasa da manema labarai, wani babban jami'in tsaron Isra'ila, Tzachi Hanegbi ya danganta halin da ake ciki a yanzu da watan Afrilun wannan shekarar, a lokacin da Iran ta kaddamar da hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami 330 kan Isra'ila. Jami'in ya ce a wancan lokacin ta ki mayar da martani ne sakamakon bukatar Amirka da kuma kawayenta, sai dai yana tunasar da Iran cewa, ramin maciji bai gaji zungura ba.

Karin bayani: Duniya ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin Israila da Iran

Hanegbi ya ce bai yi tunanin Iran za ta bari a yi fito-na-fito da juna ba. Iran da kuma kawayenta ciki har da kungiyar Hezbollah da ke Lebanon, sun sha alwashin daukar fansar kisan Haniyeh da suke zargin Isra'ila, sai dai har yanzu Isra'ila bata dauki alhakin kisan Haniyeh ba ko akasin hakan.