1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya ta samu firaminista mace ta farko

September 26, 2022

Tun bayan yakin duniya na biyu, kasar Italiya ta samu mace a matsayin wadda za ta jagoranci gwamnati. Hakan ya fito ne bayan zaben kasa da aka yi a ranar Lahadi.

https://p.dw.com/p/4HKy6
Wahl in Italien | Wahlabend in der FdI Parteizentrale
Hoto: Gregorio Borgia/AP/picture alliance

'Yar takarar jam'iyyar Brothers of Italy, Giorgia Meloni ta zama firaminista a Italiya bayan zaben majalisar dokoki da aka yi a ranar Lahadi.

Jam'iyyar ta samu akalla kashi 45 cikin 100 na kuri'un da aka lissafa, abin da ya ba ta rinjaye a majalisar.

Tuni ma dai jam'iyyar adawa da masu tsananin ra'ayi ta Democratic Party ta amsa shan kaye a zaben.

Georgia Meloni za ta kasance mace ta farko da za ta dare kan matsayin firaminista a Italiyar kuma ma daga jam'iyyarta, tun bayan Firaminista Benito Mussolini a tsakanin shekara ta 1925-1945.

Zaben na Italiya dai ya biyo bayan murabus din da tsohon firaminista Mario Draghi ya yi ne cikin watan Yulin da ya gabata.