SiyasaTurai
Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ya mutu a kurkuku
February 16, 2024Talla
Jagoran adawar Rasha Alexei Navalny, da ya yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Vladimir Putin, na fuskantar daurin shekaru 19, bisa zargin aikata laifin cin hanci da rashawa da kuma kiran gangamin adawa da manufofin fadar Kremlin.
A watan Disambar 2023, aka maida Jagoran adawar wani gidan yarin da ke yankin Artic mai tsananin sanyi da ke da nisan kilomita 1,900 daga birnin Moscow.
Tuni dai kasashen duniya suka fara martani kan mutuwar Alexei Navalny, shugaban kasar Latvia da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun bayyana mutuwar Navalny a matsayin kisan gillar da fadar Kremlin ta yi.